Daga Zahraddeen Saleh
Dukkanin shirye-shirye sun kammala a majalisar masarautar Bichi domin gudanar da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.
A wata sanarwa da aka aikowa jaridar kadaura24 mai dauke da sa hannun sakataren masarautar Bichi Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai, ta ce mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero ne zai jagoranci zaman addu’ar a ranar Juma’a 5/8/2022 a babban masallacin juma’a na garin Bichi da karfe tara na safe.

Sanarwar ta umurci dukkan malaman limamai da malaman islamiyya da na makarantun allo da ke kananan hukumomi tara na masarautar da su halarci taron.
Sanarwar ta kuma bukaci daukacin al’ummar masarautar da su halarci taron addu’o’in.

Dama dai lokaci zuwa lokaci Mai Martaba Sarkin na Bichi yakan shirya irin wannan taron don yin addu’o’in nema kasa fita dangane da kalubalen matsalar tsaro da sauran matsaloli da kasar take fuskanta.