kwana uku kenan ba’ayi karatu ba a makarantar firamare ta Aujara saboda ruwan sama

Date:

Daga Tijjani Mu’azu Aujara

 

Mamakon ruwan sama da aka kwana 3 ana yi ya hana dalibai makarantar firamare zuwa makarantar har na tsahon kwanaki uku, tare kuma da jawo afakawar bandakuna da dama a garin Aujara dake jihar Jigawa.

 

Da yake zantawa da wakilin Kadaura24 ta wayar tarho Wani mazaunin garin na Aujara Mai suna shamsudeen Bala Aujara, yace ruwa na shiga Gidaje da dama kuma ya dakatar da duk harkokin yau da kullum a garin sakamakon yawan ruwan.

Talla
Talla

 

“Yanzu hakan ma kwanaki uku kenan daliban makarantar firamaren dake Aujara Basu Sumi damar zuwa makarantar ba, saboda yadda ruwan ya cika makarantar makil, wanda hakan yayi sanadiyar dakatar da karatu a makarantar”. inji Shamsudeen

Rayuwa ta tana cikin Hadari -Hadiza Gabon

” Yanzu maganar da nake yi maka Gidan Hakiminmu ma yanzu haka saboda yawan ruwa da ke tari a Kofar Gidan ba’ a iya shige da fice a gidan tsahon kwanaki uku”. inji shi

Kofar Gidan Hakimin Aujara

Yace akwai bukatar mahukunta a jihar ta Jigawa su kaiwa al’ummar garin dauki saboda mawuyacin halin da suke cikin, Inda yace akalla bandakunan Gidaje fiye da 50 sun rufta cikin Wannan kwanaki uku.

‘Ƴan sanda na bincike kan budurwar da ta rataye kanta a Kano

Da wakilin Kadaura24 ya tuntubi Shugaban karamar hukumar ta Aujara Hon. Ado Mai unguwa Aujara yace suna iya bakin kokarisu don ganin sun samar da wasu injina da zasu rika zuke ruwan dake taruwa a makarantar don baiwa daliban damar zuwa makarantar.

Yace gwamnatin jihar Jigawa tana iya bakin kokarita don ganin an Samar da magudanan ruwa da Kuma daukar sauran matakai don gudun faruwar hakan a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...