Gwamnatin Kano da NITDA sun horar da Matasa 200 yadda zasu yi amfani da Social media don dogaro da kai

Date:

Daga Maryam Ibrahim Zawaciki

 

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa NITDA ta jaddada kudirin ta na haɗa hannu da gwamnatocin jihohi wajen ingata rayuwar matasa musamman ta fuskar amfani da kafofin sada zumunta.

 

Shugaban Hukumar na kasa Dr. Kashifu Abdullahi Inuwa ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabin a taron karawa juna sani na kwanaki biyu da suka shiryawa matasa Dari biyu bitar da hadin gwiwar ofishin Mai taimakawa gwamnan kano na musamman akan harkokin fasahar sadarwa da Kuma gudanar da gwamnati a zamanance, wanda aka gudanar a jami’ar Yusuf Maitama Sule daka Kano.

 

Dr. Kashifu Abdullahi wanda Cristiana Simon ta wakilta tace Hukumarsu ta NiTDA a shirye take ta cigaba da wayar da kan matasa kan yadda zasu yi amfani da kafafen sada zumunta wajen Gina tattalin arzikin su Mai makon sharholiya da suke yi.

Talla
Talla

 

” Aikin mune mu wayar da kan matasa domin su ribaci damammakin da suke cikin kafafen sada zumunta, saboda da yawan matasa a kasar nan suna kashe kudinsu wajen siyan data Amma Basu San yadda zasu sami kudin a shafukan da suke amfani da su ba”. inji Shugaban NITDA

 

Yace bayan Wannan damar da suka bayar ta horar da matasa Dari biyu, yace nan gaba a shirye suke su Kara fadada Shirin don bunkasa rayuwar matasan jihar Kano ta yadda zasu bada gudunmawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa.

 

A jawabinsa, mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin sadarwa da aiwatar da harkokin gwamnatin ta amfani da sadarwa Injiniya Mustapha Ibrahim ya ce an shirya taron ne domin koyawa Matasa hanyoyin amfani da kafofin sada zumunta wajen bunkasa kasuwanci su da samun kudaden shiga.

 

Ya ce gwamnati ba zata ta iya bawa kowa aiki ba, a don haka akwai bukatar Matasa su yi kokarin samawa kansu aiki ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen bunkasa tattalin arzikin kansu da kansu.

Gawuna ya zama Mukaddashin Gwamnan kano

 

“Akwai Bincike da akayi ya nuna cewa a duk Africa Nigeria ce ke kan gaba a Matasa wanda suka tashi daga shekaru 18 zuwa 35 kuma mafi yawancin su Arewacin Nigeria kuma mafi yawancin su sun fito ne daga jihar Kano, dalilin da yasa kenan muka ga dacewar mu shirya taron domin wayar da kan su yadda za su yi amfani da kafofin sada zumunta don cigaban kansu”, inji Mustapha.

 

 

Ya ce “An koyawa matasan yadda za su koma yin harkokin kasuwanci ta internet da ba tare da kaga mutum ido-da-ido ba”, “yanzu duniya ta yi cigaban dole sai ka fadada tunanin ka ta amfani da internet domin cigaban al’umma”.

 

Daga bisani yayi fatan Matasan za su yi amfani a wayoyin da suke da shi domin cigaban rayuwar su Maimakon zama Yan jagaliyar siyasa.

kwana uku kenan ba’ayi karatu ba a makarantar firamare ta Aujara saboda ruwan sama

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da Muktar Bako Getso da Aminu Dan-malam sun bayyana farin cikin su dagane da halartar taron, su na masu cewa taron yazo dai-dai a lokacin da suke bukatar sa la’akari da yadda zai taimaka musu a cigaban harkokin kasuwanci da ma bunkasa rayuwar su.

 

Shi kuwa Shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule a nan Kano Farfesa Muktar Atiku Kurawa ya ce zasu sauya Tsarin ilimin koyar da sana’o’i da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta zo da shi domin aiwatar da sana’o’in a aikace da nufin samarwa Matasa da dalibai ayyukan yi.

 

Ya ce hukumar ta zo da shirin ne domin koyawa dalibai dabarun koyon sana’o’i da nufin dogaro da Kai da kuma bunkasa tattalin arzikin matasa da kuma jihar Kano.

 

Shugaban ya ce taron wanda aka shirya da nufin nunawa Matasa dabaru da kuma hanyoyi amfani da kafofin sada zumunta na zamani kamar su Facebook da Whatsapp da Twitter da Instagram da YouTube da ma sauran manhajoji ya zo dai-dai a lokacin da ake bukatarsa la’akari da yadda dukkan masata ke amfani da kafofin sada zumunta wajen tattaunawa kawai da kuma yada wasu labaran wadanda ba za su amfane su ba.

 

Farfesa Kurawa yayi fatan mahalarta taron za su yi amfani da taron na kwanaki biyu domin samun kwarewa da dabarun da za su taimaka musu wajen cigaban rayuwar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...