Yan sanda a Kano sun kama mota dauke da Kwayoyin da kudinsu ya kai sama da Naira Miliyan 25

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar yan sandan jihar kano ta kama Wani Mai suna Abba Musa Dan kimanin shekaru 30 da haihuwa da kwayar Tramadol kimanin katan biyar wadda akadadin kudin ta yakai sama da Naira Miliyan 25.

 

An kama matashin ne a unguwar rijistar Zaki dauke kwayoyin a cikin but din mota kirar Honda Accord 2016.

 

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jami’a na Rundunar yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa kadaura24 da yammacin ranar Litinin .

Talla

” Na yarda an kamani , Amma motar ba tawa bace ta abokina ce, Mai suna Sulaiman Danwawu Mai shekaru 29 mazaunin rijistar Zaki“.

NDLEA ta rufe gidan abincin da take zargin ana sayar da kayan maye a Kano

Sanarwar tace bayan kama Sulaiman din yace motarsa ce kuma an dauko kwayoyin ne daga garin Onitsha dake jihar Anambra zuwa kano domin sayar da ita .

 

Sanarwar tace mataimakin kwamishinan yan sanda Mai kula da harkokin gudanarwa na Rundunar DCP Abubakar Zubairu ya bada umarnin a mika wadanda ake zargin da babban sashin bincike na Rundunar domin fadada bincike da Kuma gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

INEC ta rufe yiwa yan Nigeria rijistar katin zabe

 

Ya kuma ja kunne masu irin wannan dabi’a da su guji yin hakan domin Rundunar bazata saurarawa duk wanda ta kama Yana sayar da kwayoyi a jihar Kano ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...