Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza ta jihar Sokoto Isah Kalanjine, da kansiloli takwas na majalisarsa sun koma jam’iyyar APC a jihar.
Kansilolin sun hada da Zakariyya Madugu, Abubakar Kalanjine, Abubakar Aliyu, Halilu Aliyu, Ibrahim Tudu da kuma Musa Sakkwai.
Su kuwa Abdullahi Garba da Jamilu Muhammad tsoffin kansiloli ne.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, Jiya ne jagoran jam’iyyar APC, Sanata Aliyu Wamakko da kuma dan takarar gwamna a zaben 2023, Ahmad Sokoto su ka karbi wadanda suka sauya shekar, inda suka ce APC za ta yi nasara a zaben 2023.
Takarar mu da Atiku a PDP babbar barazana ce ga APC – Okowa
Sanata Wamakko ya bada tabbaci ga masu sauya shekar cewa za su ci gaba da tafiya da su wajen ci gaban jam’iyyar da ma jihar baki daya.
Ya kuma tabbatar da cewa APC za ta lashe dukkan kujerun.