Takarar mu da Atiku a PDP babbar barazana ce ga APC – Okowa

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

 

Gwamnan Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Ifeanyi Okowa, ya ce takararsu tare da Atiku Abubakar ta kasance babbar abin barazana ga APC, a zaben 2023.

Okowa na faɗin hakan ne a wani martani da ya mayarwa ɗan takarar shugabancin Najeriya a APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda yake cewa mutumin da ya zaɓa domin yi masa mataimaki ya fi na Atiku.
Gwamnan dai ya ja hankalin Tinubu, yana mai cewa ya mayar da hankali wajen tattauna batutuwa masu muhimmanci ba na mutum ba, a shirye-shiryensu na yakin neman zaben 2023.
Okowa ya ce zabin APC na ɗan takara da mataimakinsa Musulmi, ya budewa PDP kofar sa’a, saboda ‘yan Najeriya za su so ganin an yi musu adalci a matsayin tarayya.
Dan takarar ya ce Atiku Abubakar ya zabe shi ne saboda ƙwarewarsa ta siyasa, da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen gina kasa da riƙe jiharsa cikin aminci a tsawon shekara bakwai na mulkinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...