NDLEA ta rufe gidan abincin da take zargin ana sayar da kayan maye a Kano

Date:

Daga Sadiya Muhammad Sabo

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da kama kusan mutum 51 a Kano.

Hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mutanen ne bayan samun korafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurbata tarbiyar ya’yansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai sayar da magungunan jabu zuwa gidan yari na tsawoin shekaru uku, tare da biyan tarar naira 200,000.

Can ma a birnin Legas da ke Kudancin kasar NDLEA ta kama ƙwayar Tramadol sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai, da aka yi yunkurin fita da ita kasashen waje daga tashar ruwan Apapa.

NDLEA ta ce kwayar na dauke ne a cikin katan-katan 55, da suka hada da nau’ukan Tapentadol da kuma Carisoprodol na Tramadol, da kudinsu ya kai naira miliyan daya da dubu dari uku da saba’in da biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...