PDP ta lashe zaben Gwamnan jihar Osun

Date:

Aliyu Nasir Zangon Aya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ayyana Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Osun.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan cike da tsauraran matakan tsaro.

Babban baturen zaben Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya ce Sanata Adeleke ya samu kuri’a 403,371

Gwamna mai-ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’a 375,027.

Da yan Nigeria sun San halin da wasu kasashen suke cikin da sun godewa Allah – Buhari

Bayanan da INEC ta fitar na kananan hukumomi 30 da ke jihar sun nuna cewa PDP ta yi nasara a kananan hukumomi 17 yayin da APC ta samu kananan hukumomi 13.

Dama dai a baya Gwamna Oyetola, wanda ya so yin ta-zarce karo na biyu, ya kayar da Sanata Adeleke.

Wakilan BBC da ke Jihar ta Osun sun ruwaito cewa tun cikin dare ranar Lahadi zuwa wayewar gari aka fara karbar sakamakon zabukan da aka yi daga matakin kananan hukumomin jihar.

Zabar Kashim Shattima da Tinubu yayi, ya nuna zurfin tunaninsa da kuma kishin kasar nan – Rarara

Zababben gwamnan, mai shekara 62, dan asalin karamar hukumar Ede ne.

Ya wakilci yankin Osun ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party daga 2017 zuwa 2019.

Ya tsaya takarar Sanata ne bayan rasuwar dan uwansa Sanata Isiaka Adeleke.

A shekarar 2018 ya tsaya takarar gwamnan Jihar Osun amma ya sha kaye a hannun Mista Oyetola.

Ya kammala Digirinsa na farko ne a fannin nazarin aikata laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan State College da ke Amurka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...