Daga Umar Ibrahim S/mainagge
Shugaban Kungiyar tsoffin dalibai na makarantar firamare ta Goron dutse wato (Gofa) aji na shekarar 1992 Idris Sani Idris, yace sun shirya taron ya’yan kungiyar ne don taimakawa malaman makaranta da suka koyar da su da kuma sauran tsaffin daliban makarantar.
Idris Sani Idris ya bayyana hakan ne yayin taron kungiyar karo na farko wanda aka gudanar a harabar makarantar dake unguwar G/dutse .
Idris Sani Idris yace an Samar da kungiyar domin akwai malaman makaranta da suka koyar da su wadanda yanzu haka sun ajiye aiki kuma suna cikin matsaloli da suke bukatar a tallafa musu.
“Dole mu tuna da irin gudunmawar da malamanmu suka ba mu har muka zama abin da muka zama a Wannan lokaci, mun kuma San yanzu wasun su suna bukatar tallafin mu”. Inji Shugaban kungiyar
yace bayan tallafawa malaman su zasu rika tallafawa tsofaffin daliban makarantar musamman Yan ajina na 1992, saboda da mawuyacin halin da suke ciki, sannan kuma dama ce ta sada zumunci tsakanin su.
PDP ta lashe zaben Gwamnan jihar Osun
Malam Adamu Shehu Yakasai tsohon Malamin Makarantar ne ya ce sun yi farin ciki Sosai da shirya taron, Inda yace tarbiya da ingantaccen Ilimi da sukai baiwa daliban ne yasa har tsofafin daliban suka ga dacewar tallafa musu bayan sun yi ritaya.
“Abun da wadannan tsofafin daliban namu sukai mana abun a Yana ne, kuma sun tabbatar mana da cewa su yan haka ne basu manta da abun alkhairin da mukai musu ba na basu Ilimi da tarbiyya”. Inji Malam Adamu
Shi kuwa Shugaban makarantar na yanzu wato headmaster kira ya yi ga masu hannu da shuni da su tallafawa makarantar da abubuwan more rayuwa domin daliban makarantar na yanzu su sami ingantaccen Ilimi.
kungiyar ta tallafawa tsofafin malaman makaranta da kayayyakin abinci, sannan kuma sun dauki nauyin yiwa wani tsohon malaminsu aiki da ido dana mafutsara da ya dade yana fama da shi.
Taron yasamu halartar mutane daban-daban daga ciki da wajen jihar nan yayin gudanar da taron anci ansha an godewa Allah an sada zumunci.