Da yan Nigeria sun San halin da wasu kasashen suke cikin da sun godewa Allah – Buhari

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce – da ‘yan ƙasar sun san irin halin matsi da takwarorinsu na ƙasashen Afirka ke ciki – da sun gode wa Allah.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ya fadi hakan ne ranar Asabar lokacin da ya kai wa Sarkin Katsina Dr Abdulmumini Kabir Usman ziyara a fadarsa.

Ya kara da cewa ”Muna kira ga mutane da su yawaita haƙuri, muna iya bakin ƙoƙarinmu. Babu abin da ya fi zaman lafiya, muna roƙon Allah ya ba mu damar ganin bayan masu ƙoƙarin wargaza mana zaman lafiyar ƙasarmu.”

BBC Hausa ta rawaito Shugaban ya ce zai ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsa wajen yalwata wa ‘yan kasar bayan jin ƙorafe-ƙorafe kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki daga bakunan gwamnan jihar Aminu Bello Masari da kuma Sarkin Katsina.

”Da mutanenmu sun san irin halin matsin rayuwa da wasu ƙasashen Afirka ke ciki a halin yanzu, da sun gode wa Allah game da halin da suke ciki a ƙasar nan,” in ji Shugaban na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...