Mun yi Nasara yanzu Yan Nigeria suna cin Shinkafarmu ta gida bayan rufe boda – Inji Buhari

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu haka ‘yan Najeriya na cin shinkafar gida bayan rufe iyakokin kasar.

Buhari ya yabawa manoman kasar nan kan yadda suke noman shinkafa da sauran kayan abinci.

Shugaban ya bayyana jin dadinsa da yadda manufofin gwamnatin sa na noma su kai aiki yadda ya kamata.

 

Gwamnatin Kano ta rufe duk Makarantun lafiya na bogi dake jihar

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a Katsina wajen wani taro da ya gudanar da zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar.

 

Buhari ya ce yana da kyakkyawar fahimtar al’ummar Nigeria, haka tasa suka rungumi tsare-tsarensa na noma.

“Na ce dole ne mu noma abin da muke ci kuma mu ci abin da muka noma. Wannan kasa ce da ta taba dogaro da shinkafar waje a baya”.

Mun rufe iyakar mu don hana shigo da shinkafar waje. hakan tasa na ce me ya sa ba za mu cin shinkafar mu ta gida Nijeriya ba, kuma da shi nan bisa tsarin da muka yi, yanzu haka‘yan Nijeriya suna cin shinkafar gida.” Inji Buhari

 

Bakin Sallah: Yan Sanda a Kano sun kama yan daba 84 da muggan makamai

Buhari ya kara da cewa aiwatar da tsarin asusun bai daya na Treasury Single Account (TSA) ya taimaka wa gwamnati wajen dakile aiyukan jami’an gwamnati marasa kishin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...