Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta dakatar da wasu makarantun kiwon lafiya Saboda Gaza cika sharuddan da ya kamata don koyar da daliban dake da sha’awar koyar harkokin kiwon lafiya.
“Akwai abun damuwa yadda ake ci gaba da bude cibiyoyi masu zaman kansu na kiwon lafiya ba bisa ƙa’ida ba a jihar nan, ba kuma tare da bin ka’idojin kafawa da gudanar da irin waɗannan makarantu ba kamar yadda dokokin da hukumomin da abin ya shafa suka gindawa”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar yada labarai ta ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Hadiza Mustapha Namadi wadda kuma ta aikowa Kadaura24 a Kano.
“Abin takaici ne sosai yadda muka fahimci cewa ana kara samun yawaitar wasu daga cikin makarantu da takamaiman matsugunni da rashin managartan darussan da ake koyawa dalibai, sannan kuma suna kashafuka kuma suna karbar makudan kudade a wajen da iyayen dalibansu”. Inji Sanarwar
Sanarwar tace irin wadanda can makarantu suna cutar da mutane, musamman ta fuskar ci gaban ilimi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Tace Ma’aikatar tana sanar da jama’a cewa ba tare da bata lokaci ba, ta rufe duk wasu cibiyoyi na koyar da harkokin kiwon lafiya wadanda aka samar da su ba bisa ka’ida ba a jihar, har sai an kammala binciken da ya dace.
Cibiyoyin da abin ya shafa sun hada da
i.
Unity College of Health Science & Technology
Dorayi Karama (K.G/Mai), Gwale LGA
Danbatta LGA
ii.
Khalil College of Health Science & Technology
Zaria Road, Opp Gadar Lado
Darmanawa
Unguwa Uku Opp. Ofishin Hisbah
Karkasara, Opp. Masallacin Bilal, Tarauni LGA
Danbatta LGA
Wudil LGA
iii.
Shamila College of Health Science & Technology
Gezawa LGA
iv.
Autan Bawo College of Health Science & Technology
Rano LGA
v.
Kwalejin Amincewa ta Kimiyya da Fasaha ta Lafiya
Jakara, Dala LGA – Kano
Bachirawa, Ungoggo LGA – Kano
vi.
Eagle College of Health Science & Technology
Bichi LGA
vii.
Albakari College of Health Science & Technology
Rijiyar Zaki, Ungoggo LGA – Kano
viii.
Jamatu College of Health Science & Technology
Kura LGA
ix.
Savanna College of Health Science & Technology
Wudil LGA
x.
Cibiyar Ilimin Lafiya
Ahmadiyya, Opp. Ofishin INEC
xi.
Jamilu Chiroma College of Health Science & Technology
Kings-Garden, Zungero, Opp. Titin filin jirgin sama, S/Gari
xii.
Sir Sanusi College of Health Science & Technology
Matan Fada Road
xiii.
Aminu Ado Bayero College of Health Science & Technology
Ado Bayero Layout, Dandinshe Yamma – Dala LGA
xiv.
Awwab College of Health Science & Technology
Salanta, Gwale LGA
xv.
Gwarzo Unity College of Health Science & Technology
Gwarzo LGA
xvi.
Al-wasa’u College of Health Science & Technology
T/Fulani, Nassarawa LGA – Kano
xvii.
Kanima Academy
Layin Dan-kargo, Zangon Dakata, Nassarawa LGA – Kano
xviii.
Muslim College of Health Science & Technology
Zungeru Road, Fagge LGA – Kano
ku xix.
Utopia College of Health Science & Technology
Jigirya JSS, Yankaba, Nassarawa LGA – Kano
xx.
Jama’a College of Health Science & Technology
Na’ibawa Yan-lemo, Tarauni LGA – Kano
xxi.
Kausar Healthcare Academy
Jos Road, Beside Islamic Centre, T/Wada LGA – Kano
xxii.
Shanono College of Health Science & Technology
No. 33 Kofar Gari, Shanono LGA – Kano
xxiii.
Cibiyar Ilimin Kiwon Lafiya ta asali
Jakara Guarden, Airport Road, Nassarawa LGA – Kano
xxiv.
Makarantar Fasaha ta Lafiya
Habib Faruq Girls Sec. Sch., Gidan Kara, Kurna T/Fulani
xxv.
Makarantar Fasaha ta Lafiya
Bachirawa Special Primary School, Ungoggo LGA
xxvi.
Fudiyya School of Health Sciences
Danrimi, ‘Yan-babura Rijiyar Lemo, Fagge LGA
Ma’aikatar za ta hadin kai da duk hukumomin da ke da ruwa da tsaki don tabbatar da sanya ido akan duk cibiyoyin koyar da harkokin lafiya a fadin jihar Kano domin samun lafiya da kwanciyar hankali.