Mun gaji da yajin aikin da jami’o’i ke yi a Nigeria, ya kamata a kawo ƙarshen shi cikin gaggawa – Auwal Danlabarawa

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation tayi Kira da kaukausar Murya ga Gwamnatin Nijeriya akan warware matsalar data janyo dogon yajin aikin jami’oi a ƙasar dan sharewa yan kasa da suke marasa karfi a makarantun gwamnati.

 

Shugaban gidauniyar Amb. Auwal Muhd Ɗanlarabawa yace halin da ake ciki ya damu al’umma iyaye da su kansu matasa da suke Ɗalibai a wadannan makarantu duba ga halin ko in kula da ake nunawa a yajin aikin da malaman jami’a na ASUU ke yi.

 

Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso

 

Ɗanlarabawa ya Kara da cewa Halin da ake ciki yanzu dai yajin aikin ASUU ya shiga wata na biyar, sannan babu labarin komawa makarantu domin har yanzu an kasa cimma matsaya tsakanin malaman da gwamnatin tarayya.

 

Amma hakan bai Hana gudanar harkoki na siyasa da kashe makudan kuɗaɗe a bangaren ba, an bar matasa a gari ba karatu ba Aikinyi, sannan Kuma an ruguza musu lissafinsu na kammala makaranta Akan lokaci tare da tafiya yajin aikin da ba’a San lokacin denawa ba.

 

2023: Atiku Abubakar ya bada tallafin Naira Dubu Hamsin-Hamsin ga Mata a Kano

 

Wannan ba karamin kalubale bane a kasar, sannan Kuma tarnaki ne ga makomar Matasan da Kuma zaman lafiya a ƙasa duba ga halin da ake ciki na rashin tsaro Wanda aka Daɗe ana kokawa dashi Kuma har yanzu ba’a samo nasarar dakilewa ba.

 

“Muna Kira da Gwamnati data gaggauta sasantawa tare da kawo ƙarshen wannan yajin Aiki, yadda makarantun zasu koma aiki Kuma ya Zama Daga wannan lokacin ba’a sake samun wata baraka da zata haifar da sake samun yajin Aiki a ƙasar Nan ba”.

 

Ƙarshe babu wata Gwamnati dake son kasancewar Ƴan kasarta su Shiga Tashin Hankali na kasa cimma burinsu na yin karatu, sannan Kuma ya Zama wajibi Gwamnati ta duba rahotanni da ake dasu na aikata manyan laifuka a wannan lokaci da yadda suke karuwa duk hakan yana da nasaba da wannan illar da akayiwa Matasan na rashin cimma burinsu na samun ilmi da zuwa makaranta.

 

Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa ya godewa ɗaukacin Jakadun cigaban al’umma ( Grassroot Community Development Ambassadors ) da suke ta ƙoƙarin wayar da Kan Matasan wajen ganin Basu faɗa cikin muggan manyan laifuka ba, tare da Basu hakuri da cigaba da addu’a Allah ya kawo Ƙarshen wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...