2023: Hada Musulmi da Musulmi da APC ta yi Babban Kuskure ne – Babachir

Date:

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Babachir Lawal, ya ce zabin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahgmed Tinubu ya yi na Musulmi a matsayin mataimakinsa gagarumin kuskure ne.

 

Lawal, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da Kansa a ranar Talata, inda yace daukar wannan matakin kuskure ne babba.

 

Babachir ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, inda yake ganin illar hakan kasancewar Tinubun shi ma Musulmi ne.

 

A ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa 2023.

 

Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda ya mara wa Tinubu baya a zaben fitar da gwani na APC, ya ce zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka

 

Ya ce bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewar ne suka sa hakan , da cewa ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.

 

Ya yi gargadi da cewa, ”Idan har Tinubun yana ganin wannan zabin shi zai ba shi nasarar samun kuri’un Musulmin arewa, to ya yi kuskure.”

 

”Saboda za su yi tururuwa su zabi daya daga cikin ‘ya’yansu ne, saboda haka al’adarsu take” In ji shi.

 

”Buhari, wanda shi ne dansu na fari ba zai kasance dan takara ba a 2023. Amma Atiku dansu na biyu zai kasance.” In ji Babachir.

 

Saboda haka Tsohon Sakataren yana ganin Atiku Abubakar dan takarar babbar jam’iyyar hammaya, PDP, ‘yan arewa za su zaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...