Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Shugaban kungiyar tsofafin Daliban makarantar sakandire ta Stadium wato (STOBA) Alhaji Kabiru Ibrahim Gidan Kara ya bukaci kungiyoyi irin nasu dasu Maida hankali wajen kaiwa makarantar su cigaba, ta hanyar Amfani da damar gina shiguna a jikin makarantu da gwamnati ke yi a wannan lokaci.
Alhaji Kabiru Ibrahim Gidan Kara ya bayyana hakan ne yayin taron kungiyar tsofafin Daliban makarantar sakandire ta Stadium wanda aka gudanar a harabar makarantar dake kan titin Airport Road a Kano.
Yace makarantar sakandire ta Stadium ta amfani tsarin Gina shiguna a jikin makarantar sakamakon hanyoyin da suka bi na tattauanawa da gwamnati kafin a fara aikin shagunan.
Gidan Kara yace a tattauanawarsu da gwamnati sun fada mata cewa makarantar tana bukatar sabbin gine-gine da kuma gyaran wadanda suka lalace wanda suke bukatar gwamnati ta gyarasu gabanin fara aikin ko kuma idan an fara aikin Gina shigunan.
” baza ka iya hana gwamnati ta yi abun da ta yi niyyar yi ba, tun da makarantar tata kai ma kuma nata ce nata ne, wannan tasa bamu tada hayaniya ba lokaci da za’a yin Amma dai mun fadi buƙatun mu kuma duk an yi mana”. inji Gidan Kara
Kabiru Gidan Kara yace a sanadiyar aikin Gina shigunan an gyara mana azuzuwa kusan kimanin guda takwas wadanda suka kone shekara tara da suka gabata, sanann an gyara mana bandakin da ya dade da lalacewa ,sa’annan an Kara tsayin katangar makarantar saboda barayi suna shiga don yin sata, da dai Sauran aiyuka da dama.
Shugaban na STOBA yace bayan ga wadancan aiyuka wasu daga cikin shugabannin makarantar suna taimakawa makarantar da aikace-aikace koma gyare-gyare, Inda ya bada misali da aiyukan da Shugaban karamar hukumar Nasarawa Auwal Aranposu ya yi da dai sauransu.

A nasa jawabin shugaban kungiyar iyayen yara da Malamai ta makarantar Alhaji Musa Garba Gawuna ya ce bai kamata kungiyoyin dalibai su rika kokarin yin fada da gwamnati ba, Inda yace a sanadiyar masalaha makarantar sakandire ta Stadium ta samu aiyukan Cigaba Mai yawa .
Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso
Shima a jawabinsa shugaban makarantar na yanzu ya yabawa kungiyar tsofafin Daliban makarantar saboda irin gudunmawar da suke baiwa makarantar wajen cigaban ta, Inda ya yi fatan sauran kungiyoyi zasu yi koyi da salon gudanarwar kungiyar tsofafin daliban ta Stadium.