Bikin Sallah: Masu bukata ta Musamman a kano sun kai ziyara ga masu lalurar laka

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

 

Hadaddiyar kungiyar dukkanin masu bukata ta musamman reshen jihar Kano, ta kai ziyarar duba marasa Lafiya musamman masu fama da lalurar laka a babban Asibitin kashi na dala da kuma yi musu barka da sallah .

Da yake jawabin shugaban kungiyar Hon Yakubu Sunusi, yace sun shirya gudanar da ziyarar ne domin neman lada a wajen Allah, da kuma bada tasu gudunmawar ga Masu lalurar ta laka musamman a Wannan Lokaci na bikin Sallah Babba.
Shugaban kungiyar wanda mataimaki na musamman ne ga shugaban karamar hukumar Nasarawa, yace a irin wannan lokaci akwai bukatar al’umma su rika zuwa asibitoci don duba marasa Lafiya da kuma taimaka musa don su ma su ji cewa an damu da halin da suke cikin.
“Mun Kawowa wadannan mutane ziyarar ne a wannan lokaci saboda mu sanya farin ciki a zukatansa kuma mu tallafa musu da Dan abun da Allah ya hore mana,saboda wasun mu sun zauna a wannan wuri lokacin suna jinya don haka mun San halin da mutum yake ciki idan Yana wannan wurin”. Inji Yakubu Sanusi  
Shugaban kungiyar ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da masu mukamai da su kara kokari wajen ganin sun taimakawa masu bukata ta musamman a kowanne irin lokaci domin Neman lada a wajen Allah madaukakin sarki.
 A nata jawabin wata Babbar jami’ar Asibitin Mai suna Hajiya Binta Mukhtar ta baiyana farin cikin ta da wannan abun alkhairi da yan kungiyar sukai gudanar tare da gode musu da kuma bada tabbacin Asibitin zai cigaba da baiwa marasa Lafiyar kulawar data dace.
Ta ce da sauran kungiyoyi zasu rika bada irin wannan tallafi ga Masu fama da irin wannan lalurar ta laka dama sauran majinyara Babu Shakka da an sami gagarumin cigaba.
Kungiyar dai ta rabawa marasa Lafiyar Naman Sallah domin suma ji ci kamar yadda kowanne dan Adam yake ci a wannan lokaci na Bikin Sallah babban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...