Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta Wani labari dake cewa Sanata Kwankwaso wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaben 2023 ya amince Magoya bayansa su zabi Asiwaju Bola Tinubu.

 

Kwamitin yakin neman zaben bayyana karara cewa Sen. Rabiu Musa Kwankwaso yana nan daram ya na takararsa ta shugaban kasa kuma bai ce yana marawa Wani Dan takara baya ba.

Hawan Nasarawa:Ganduje ya bayyana dalilin da yasa bai tarbi Sarkin Kano a gidan gwamnatin ba

 

Domin samun cikakken bayanin da kaucewa shakku, nemi hirar da Kwankwaso yayi a Arise TV da Dr. Reuben Abati, Inda ya tambayi Sen. Kwankwanso ra’ayinsa game da Asiwaju Bola Tinubu. Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana karara a amsar da ya bayar cewa “Bola Tinubu abokina ne shekaru da dama, da ban tsaya takara ba, da na mara masa baya, Amma yanzu mu biyun duk muna takarar shugaban kasa ne ta ya zan goyi bayansa”. A cewar kwankwaso

 

 

A Cikin sanarwar da hadimin kwankwason kan harkokin yada labarai Muyi Fatosa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24, yace kwamitin ya yi martani da kakkausar murya kan rahoton, Inda yace Rabi’u Musa Kwankwaso ta kowace fuska ba zai mara baya Bola Tinubu ba, ya kuma bukaci jama’a da su tabbatar da sahihancin duk wani abu da suke gani a kafafen yada labarai.

Duk da gudunmawar da Masu sana’ar dabbobi suke bayarwa, Amma bama samun tallafin gwamnati – Mustapha Ali

Kwamitin ya kuma ja hankalin masu ruwa da tsaki da ‘yan jam’iyya da magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da su yi watsi da rahotannin karya da ake yadawa a shafukan sada zumunta tare da ci gaba da marawa wanda ya dace a wannan aiki Sanata Kwankwanso baya ta kowace hanya.

 

Ana ci gaba da tuntubarmu a duk jihohin tarayyar kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya, kuma ya zuwa yanzu, ra’ayoyin Magoya bayan na Kara mana kwarin gwiwa.

Har yanzu muna kara tabbatar wa ‘yan Najeriya da jiga-jigan magoya bayan Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, cewa Sen. Kwankwanso har yanzu shi ne dan takarar da muka sa a gaba kuma zai ci zaben shugaban kasa na 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...