Daga Hauwa Aliyu
Dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya taya dalukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Sallah Babba.
A wani sako da ya rabawa manema labarai, Tanko ya ce bikin Sallah Babba ya tunatar da 1 kai a tsakanin su.
Ya ƙarfafa musu gwaiwar su ci gaba da fadakar da junansu kan muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai.
2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu
Salihu Tanko Yakasai ya kuma nuna farin cikinsa da irin tarbar da masarautar Rano ta yi masa a lokacin da ya je Masarautar domin yin Sallar idi tare da Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Muhd Kabir Inuwa.
“Ina yi wa musulman Kano da Nijeriya baki daya fatan anyi Sallah Lafiya, ina rokon su da su kasance Masu son hadin kai da zaman lafiya a tsakanin su, su yi addu’a ta musamman ga kasar nan saboda kalubalen da take ciki.
2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu
“Har ila yau, ina mika godiya ta musamman ga Majalisar Masarautar Rano da ta karbe mu, kuma a cewarmu, sun yi mana kyakkyawar tarba, muna godiya sosai.
Tanko ya yi kira ga kowa da kowa da su karbi katin zabe na dindindin domin samun damar zaben shugabanni masu gaskiya a zabe mai zuwa.