2023:Ka kula da lafiyarka, domin kamfedin bana Mai wuya ne – Kwankwaso ya fadawa Tinubu

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya shawarci dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya kula da lafiyarsa gabanin shiga zaben 2023.

Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne kuma wanda ya mulki jihar Kano sau biyu, yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Lahadi, ya ce kamata ya yi Tinubu ya kula da lafiyarsa, inda ya yi gargadin cewa yakin neman zaben 2023 zai kasance da tsauri.

“Idan ka ga abokina Bola, ka ce masa ya bi a sannu, ya kula da lafiyarsa sosai… saboda ina sonsa sosai, abokina ne.

“Wannan yakin neman zaben zai yi tsauri sosai, yana bukatar jajircewa sosai da dai sauransu. Ina fatan zai yi sauki domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa daya mai karfi da wadata a Nijeriya,” in ji Kwankwaso.

Da aka tambaye shi ko Tinubu na masa barazana, Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar wakilai a jamhuriya ta uku, ya ce Tinubu a matsayinsa a kashin kansa mutumin kirki ne amma bai san abin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai yi daban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

“Damuwata kawai ita ce jam’iyyar da ya fito. Na san shi mai dabara ne, Bola Tinubu, mutumin kirki ne. Na zauna tare da shi sau da yawa ba za a iya kirgawa ba daga 1992 zuwa yau.

Da dumi-dumi: Tinubu ya zabi tsohon gwamnan Borno a matsayin mataimaki

“Ina fatan idan gan shi zan tambaye shi me zai gaya wa ‘yan Nijeriya abin da zai yi na daban da abin da Muhammadu Buhari ke yi a yau.

“Wannan ita ce babbar damuwata a gare shi. Idan ba yi nasara ba, zan iya ba shi shawara amma zai zama kamar gina wani abu ne bai mai billewa ba.

“Idan na gan shi, zan yi masa fatan alheri ko kuma idan kun gan shi, ku ce masa ina yi masa fatan alheri – amma ya bi a sannu,” in ji Kwankwaso.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne Tinubu ya bayyana zabar tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shetima a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya haifar da cece-kuce a kan cancanta ko kuma rashin cancantar takarar mutum biyu data addini daya idan aka yi la’akari da kasancewar Nijeriya na da mabambamtan addinai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...