Daga Aisha Aliyu Umar
Dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu ya sanar da Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin wanda zai masa mataimaki a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu ya sanar da hakan ne yayin tattaunawarsa da manema labarai a jihar Katsina, jim kaɗan bayan ziyarar Sallah da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“jiga-jigan jam’iyyar APC, an zabi Shettima ne saboda tsohon gwamnan jihar Borno ne kuma yana da “Kwarewar aiki, kuma mutum ne da kowa zai aminta da shi hakan tasa na zabe shi a matsayin abokin takarata”. Inji Tinubu
An jima dai ana kai ruwa rana kan wanda zai zama mataimakin sa a takarar shugaban kasa da yake yiwa jam’iyyar APC.
Kawu Sumaila ya taya al’ummar Musulmi Murnar Sallah Babba, ya bakuci su hada Kai
Idan ba’a manta ba, Kadaura24 ta rawaito ko a ranar juma’ar data gabata sai da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce su suka baiwa Tinubun shawarar ya dauki Musulmi a matsayin mataimakin sa duk kuwa da kalubalen da zasu fuskanta.