Rahotanni sun bayyana cewa, Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya amince da ɗaukar Musulmi a matsayin mataimakin takararsa.
A shirye nake na gudanar da aiyukan Cigaba Kano Idan na zama Gwamna 2023 – Abba Gida-gida
Wata majiya mai ƙarfi a Ƙungiyar Yakin neman zaben Tinubu, wacce ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa da NAN hakan a yau Lahadi a Abuja.
Ganduje ya yiwa fursunoni sama da 3,800 afuwa cikin Shekaru 7
Majiyar ta shaida wa NAN cewa Tinubu zai bayyana sunan mataimakin takarar a wannan makon.
A makonnin da suka gabata, an yi ta muhawara a ƙasa kan addinin ƴan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje dama yace su ne suka baiwa Tinubun shawarar ya dauki Musulmi a matsayin mataimakin sa a takarar shugaban kasa da yake yi was jam’iyyar APC.