Daga Kamal Yahya Zakaria
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPPa Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya tabbatarwa da al’ummar jihar nan cewa a shirye yake ya gabatar da aiyukan Cigaba a fadin jihar idan har aka zabe shi a matsayin gwamna a shekara ta 2023.
Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan a sakon sa na Barka da Sallah ga al’ummar jihar kano.
Ganduje ya yiwa fursunoni sama da 3,800 afuwa cikin Shekaru 7
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin addu’o’in don idan sun hau mulki su dawo da shugabanci nagari, bin doka da oda da kuma yin kyakyawan shugabanci a kowanne bangarorin .
2023: Wani Malami a Kano ya yi tallan Kwankwaso a filin Sallar idi
Dan takarar gwamnan ya ce yana da tsarin da zai samar da jindadin ga jama’a,ma’aikatan gwamnati yan fansho da dai Sauran al’umma baki daya a jihar kano.
Abba Kabir ya taya dukkanin al’ummar jihar kano Barka da Sallah da fatan Allah ya maimata mana.