Daga Haleema Umar Sabaru
Shugaban kwamitin bita na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Sheikh Harun Muhd Sani Ibn Sina yace maniyatan jihar nan da basu Sami zuwa kasar Mai tsarki su dauka cewa haka Allah ya kaddara musu, kuma akwai kyakyawan yakinin zasu Sami ladan niyyar da sukai.
Kadaura24 ta rawaito Sheikh Harun Ibini Sina ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a nan Kano.
Shugaban kwamitin bitar wanda shi ne kwamandan Hisbah na jihar Kano yace kamata yayi maniyatan su Mai da lamarin su ga Allah, su dauka cewa haka ya tsara kuma babu wanda ya Isa ya sauya hukunci Allah.
Yace abun da ya faru suma basu ji dadin faruwar sa ba, kuma hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta yi iya bakin kokarinta don ganin an kwashe dukkanin maniyatan jihar Kano Amma lamarin yaci tura.
Yace yanzu haka Shugaban Hukumar Jin dadin alhazai ta Kano Farfesa Sale Pakistan bai Sami tafiya ba, Sakataren zartarwar hukumar ma haka da dai Sauran daraktocin Hukumar,duk da suna da damar zuwa, amma sun hakura saboda jimamin abun da ya faru ga maniyatan jihar Kano Dana wasu jihohin.
Sheikh bn Sina yace duk da basu je saudiyyan a bana ba, Amma sun gudanar da kyakyawan tsarin yadda za a cigaba da yiwa Mahajjatan Kano bita har a kammala Ibadar aikin Hajjin ta bana.