Ganduje ya yiwa fursunoni sama da 3,800 afuwa cikin Shekaru 7

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 90 afuwa ciki har da mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa.

 

Gwamnan ya aiwatar da hakan ne sakamakon bikin Babbar Sallah.

 

Gwamna Ganduje, ya biya wa mutum 77 diyyar kuɗin da ake binsu domin fita daga gidan gyaran halin haka kuma akwai mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa a baya da halayansu aka gamsu da su wanda hakan ya sa gwamnan ya yi musu afuwa.

 

Haka kuma akwai fursunoni uku da aka yanke wa hukuncin kisa da gwamnan ya yi musu afuwa aka mayar da hukuncinsu ɗaurin rai da rai.

 

Gwamna Ganduje ya kuma bai wa fursunonin shanu da raguna da shinkafa domin su ji daɗin Babbar Sallah.

 

Muna fatan Zamu cigaba da irin wannan aikin musamman idan Allah yasa mataimakina Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya zama Gwamnan jihar Kano a shekara ta 2023″. inji Ganduje

 

kadaura24 ta rawaito cewa cikin Shekaru 7 da suka gabata Ganduje ya yiwa fursunoni 3,898 afuwa a lokuta irin wannan na Sallah Babba da Karama.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...