Daga Kamal Yahya Zakaria
Allah ya yi wa wata mahajjaciya yar jihar Kaduna rasuwa a yau a filin Arafat da ke birnin Makkah
Kadaura24 ta rawaito Wacce ta rasun Mai suna Hasiya Aminu daga karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna ta rasu ne a filin Arafat jim kadan bayan ta gama taimakawa wajen rabon abinci ga alhazai a tanti dake filin na Arafa.
Bayan Gaza kammala jigilar maniyatan Nigeria, NAHCON ta Nemi afuwar Gwamnati da Yan kasar
Da yake tabbatar da rasuwarta, mukaddashin Daraktan ayyuka na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Abubakar Alhassan ya ce a safiyar yau marigayiyar na daga cikin ne alhazan da suka je Jabbal Rahma (dutsen rahama) inda suka koma tantinta.
Za a fara kidayar gwaji ranar 11 ga wata Yuli a Kano – NPC
Yace ta rasu a cikin tanti ba tare da wani ciwo ba