Mu muka baiwa Tinubu shawar ya dauki Mataimaki Musulmi, kuma ya Amince – Ganduje

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace su ne suka baiwa Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu shawarar ya dauko mataimaki Musulmi duk da abun ne Mai wuya.

Yace sun bashi shawarar kuma ya Amince zai dauki Mataimaki Musulmi duk da dai an Saba da ganin shugaba Musulmi mataimaki kirista ko shugaba kirista mataimaki Musulmi.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin addu’o’i na musamman da gwamnatin jihar kano ta shirya domin yiwa jihar nan addu’ar samun Zaman lafiya a wannan rana ta Arfa.

“Mu muka baiwa Tinubu shawarar ya dauki Musulmi saboda mu muka Fi su yawa in yaso ko ma Mai zai faru ya faru, wanda zai zabe mu ya zabe mu,wanda kuma bazai zabe mu ba ya riƙe kuri’arsa kuma Tinubun ya yarda da shawarar tamu”. Inji Ganduje

Ganduje yace suna da kwarin gwiwar cin zaben shugaban kasa a 2023 musamman idan muka hada Musulmi da Musulmi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...