Daga Auwal Alhassan Kademi
An yi ta yaɗa bidiyon wata ƴar hatsaniya da ta faru a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin Najeriya, lokacin da shugaban hukumar alhazai ta jihar Neja Umar Makun Lapai ya hana shugaban hukumar alhazai ta kasar NAHCON Zikrullah Hassan hawa jirgi don zuwa kasar Saudiyya.
Umar Makun Lapai ya tabbatar da faruwar lamari, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai daga Minna babban birnin jihar Neja.
Ya ce ba zai iya barin Shugaban Hukumar na kasa ya tafi aikin hajji ba yayin da kashi hamsin cikin dari na maniyyatan jihar Neja da sauran jihohin Najeriya ke nan a makale.
Hajjin bana:Kasar Saudiyya ta karawa Nigeria Wa’adin Kai Maniyatan ta zuwa kasar
Ya ce a matsayinsa na shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, bai kamata Zikrullah Hassan ya kama hanya ya tafi aikin Hajjin yayin da adadin maniyyata da dama da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya basu san makomarsu ba a bana.
A cewarsa kamata ya yi a ce shugabanni ne za su kasance na karshe da za su tafi aikin hajji domin tabbatar da cewa ba a bar wani maniyyaci a baya ba.