Hukumomin Saudiyya sun sanar da ƙarin lokacin jigilar alhazai zuwa kasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar aikin hajji na Najeriya ta fitar, ta ce matakin zai kwatar da hankalin aƙalla maniyyatan Najeriya kusan 3000 da suka maƙale.
Ta ce hakan ya biyo bayan doguwar tattaunawa tsakanin Najeriya da Saudiyya, karkashin jagorancin shugaban hukumar Zikrullah Hassan.