Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Kungiyar APC Media forum, yan jam’iyyar APC masu magana a kafafen yada labarai sun gudanar da zabe a yau talata Inda suka zabi Sale Kala Kawo a matsayin Sabon zababben shugaban kungiyar.
An gudanar da zaben ne karkashin kulawar jam’in zabe Ahmad Musa wanda shin ya bayyana sakamakon zaben bayan an kammala kada Kuri’u kamar yadda kundin tsarin kungiyar ya tanada .
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da bullar cutar Kyandar Biri a jihar
Ahmad Musa yace Sale Kala Kawo shi ne ya lashe zaben da Kuri’u guda 76 wanda hakan ta nuna shi ya Sami kuri’a Mafi rijiye kuma ya cika dukkanin ka’idojin zabe don hakan” Na ke tabbatar da cewa Sale Kala Kawo shi ne sabon zababben shugaban wannan kungiyar ta APC Media forum”.
Chairman Hon Sale kala Kawo
Mataimakiyar sa Hannatu Abdulkadir ta
Sakataran kungiya Hon Umar Mai Rice
Ma’ajin kungiya Shamsu Mai Shadda
Shugaban Mata Karimatu Musa Matashiya
Sakataran Tsare Tsare Adamu Danjuma Isa
Sai kuma Hon. Abdullahi Maikano Zara na daga cikin iyayen kungiya.
A zantawarsa da wakilin kadaura24 bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Sale Kala Kawo ya bukaci sauran ‘ya’yan kungiyar wadanda suke adawa da bangarensu dasu zo su hade don ciyar da kungiyar da jami’ar APCn Kano gaba.
Na yi alkawari shirya sahihin zaben Kungiyar APC Media forum ta Kano – Ibrahim Maishinku
Sale Kala ya godewa duk shugabannin kwamitin da suka shirya zaben bisa dattako da suka nuna, sannan kuma ya yabawa wakilan jami’an tsaro wadanda suka halacci zaben don ganin ya gudana lafiya.
Sale Kala Kawo dai ya taba riƙe shugaban kwamitin rikon kungiyar a baya ganin ya sauka har aka shirya zaben da ya bashi Nasara. Inda a gefe guda kuma wasu yan kungiyar nacan suna shirin shirya wani zaben don zabar wasu shugabannin.