Daga Sayyadi Abubakar Sadiq
Wani Dan kishin kasa kuma Mai rike da sarautar Falakin Shinkafi Ambasadan Zaman lafiya Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya hori al’ummar jihar kano dana kasa baki daya da su himmatu wajen yashe magudanan ruwansu don gudun ambaliyar ruwan sama.
Yace barin magudanan ruwa ba tare da yashe su ba, musamman a wannan lokaci na damuna yana da hadari sosai saboda shi yake kawo ambaliyar ruwan sama
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bayyana hakan ne yayin wata ganawarsa da wakilin kadaura24 a safiyar talatar nan .
Yace ya kamata mutane su daina jiran sai gwamnati ta zo ta yi musu yasar magudanan ruwa a unguwannin su, saboda abubuwa su yiwa mata yawa kuma idan aka tsaya jiranta abun da ba’a fata ya faru.
“ku kuke zaune a unguwannin ku kuma idan matsala ta zo ku Zata fara shafa, domin kune zaku yi asarar rayuka da dukiyoyin ku, don haka ku yafi dacewa ku taimakawa kanku don kaucewa waccen matsalar.” inji Falakin Shinkafi
Amb. Yunusa Yusuf yace kamata yayi gwamnati da masu ruwa da tsaki a kowacce unguwa su baiwa yashe magudanan ruwa muhimmanci ko a rage afkuwar ambaliyar ruwan sama a Cikin al’umma.
kadaura24 ta rawaito Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya kan je unguwar su ta Yakasai a duk asabar din karshen wata, domin shiga Cikin matasan da suke aikin yashe magudanan ruwa unguwar don karawa matasan kwarin gwiwar tsaftace yankin nasu