An farwa yan Majalisar dokokin jihar Bauchi a wurin shakatawarsu

Date:

Daga Kamal Yahya Zakaria

 

A jiya Litinin ne dai wasu ɓata-gari su ka kai wa ƴan majalisar dokokin Jihar Bauchi farmaki a gidan shaƙatawarsu, inda su ka raunata mutum shida tare da lalata motoci da tagogi a gidan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa majalisar ta faɗa cikin rikicin shugabanci inda a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne mambobi 22 su ka kaɗa ƙuri’ar rashin goyon baya ga shugaban majalisar, Abubakar Suleiman da sauran masu riƙe da muƙamai a majalisar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Babale Abubakar, ya shaida wa manema labarai a jiya Litinin a Bauchi cewa, harin da ya faru da misalin karfe 4 na yamma, a daidai lokacin da ƴan majalisar ke gudanar da taro, ya yi sanadin jikkata shida daga cikinsu.

“Akalla motoci shida maharan suka lalata da su kuma suka fasa gilashin tagogi.

“Sun fi 100 kuma suna ɗauke da bindigogi, kokara da adduna,” in ji shi.

“Abin ban tsoro ne. Wasu daga cikin mu sun gudu zuwa kofar fita kuma sun ji rauni sosai,” in ji shugaban masu rinjaye.

“Al’amari ne mai ban tsoro. Abin bakin ciki ne,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...