Daga Ibrahim Sani Gama
An bayyana tsadar da dabbobi suka yi a kasuwanni da cewa hakan ta faru ne sakamakon kudaden da masu kiwo suke kashewa wajen ciyar da dabbobin.
Shugaban kungiyar masu fataucin dabbobin ta kasa Alhaji Mustafa Ali ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake kano.
Alhaji Ali Ya bayyana cewar abaya kiwata rago kan lashe kudi kimanin Naira dubu 20 a watannin 4, amma yanzu abin ba haka yake ba kasancewar kiwata rago kan lashe kimanin naira dubu 30 a wata saboda tsarin kiwo Zamani.
Ya kuma bayyana cewar daga raguna har shanu tsarin kiwon su daya ne don haka yace a yanzu haka duba da karatowar lokacin babbar sallah ya tsaya a tsaka- tsaki wato bai karu ba kuma bai raguba.
Kazalika Shugaban kungiyar ya baiwa al’umma tabbacin cewar zasu shiga lamarin wajen dai-daita farashin dabbobin a kasuwanni don al’umma su sami damar yin layya cikin sauki.
Ya kuma yi kira ga al’umma da cewa kada su ga baiken masu kiwon dabbobi, kasancewar kungiyar su na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta dai-daita farashin dabbobin a kasuwanni.
Alhaji Mustafa Ali Ya kuma yi Kira ga masu sayar da dabbobi a kasuwanni da su sassauta farashin dabbobin su don al’umma su samu damar yin layya cikin sauki, tare da kaucewa sanya dogon buri a farashin dabbobin su.
Ya kara da cewar tsakanin farkon watan daya wuce zuwa farkon wannan watan kungiyar ke yin tafiye tafiye zuwa Sassa daban-daban na kasar nan domin dai-daita al’amuran da zasu taimaki kungiyar su da kuma al’ummar kasar nan.
Ya kara da Cewar yayin tafiye tafiyen nasu sai da suka tabbatar cewar dabbobin da suka rarraba sun riski sassa daban daban na kasar nan.
Shima anasa bangaren mataimakin Shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyyar kudancin kasarnan Muhammad sani Abdullahi yace Ayarin kungiyar su ya kai ziyara jihohim Abiya da Oyo da Ebonyi da sauran jihohim da rikici Ya rutsa da ya’yan kungiyarsu, inda suka kulla yarjejeniya da kuma samun tabbacin baiwa ya’yansu damar gudanar da kasuwacinsu cikin kwaciyar hankali.
Daga karshe Shugaban kungiyar na kasa ya yi kira ga yayan Kungiyarsu kan su kwantar da hankalin su kuma su zauna da al’ummar yankunan da suke gudanar da kasuwancin su lafiya musamman ma kudancin kasarnan.