Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sen Uba Sani ya zabi Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa Uba Sani ya fitar ranar Litinin kamar yadda jaridar solacebase ta rawaito.
“Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zabi mai girma mataimakiyar Gwamna, Dokta Hadeeza Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna,” in ji sanarwar.
Majiyar Kadaura24 ta ruwaito cewa Hadiza Sabuwa Balarabe, ita ce mataimakiyar gwamnan Nasir El-Rufai a halin yanzu
“Dr. Hadiza Balarabe ta ba da gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a jihar.
“Dr. Balarabe ta nuna kwazo sosai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na mataimakiyar Gwamna wanda ya kara mata daraja a cikin masu ruwa da tsaki a jihar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Don haka ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata. Na kuma bukace ku da ku fito ranar zabe don kada mana kuri’a yayin babban zaben 2023 mai zuwa. Zabar mu a 2023 zai ba mu damar gina jihar Kaduna cikin lumana, wadata, da kuma girma.