Daga Abdulrashid B Imam
Shugaban karamar hukumar kumbotso, Alhaji Hassan Garba Farawa ya mika sakon ta’aziyya ga babban sufeton ‘yan sandan kasar nan, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da daukacin jami’an tsaro da ke aiki a yankin bisa rasuwar ADC Junaidu Ayuba. wanda ya rasu bayan fama da matsalar koda na tsawon lokaci.
Shugaban wanda ya nuna alhininsa bisa ga rasuwar Dogarin nasa, sannan mika sakon ta’aziyyar ga iyalai da yan uwan mamacin.
Cikin wata sanarwa da hadimin shugaban karamar hukumar kan harkokin yada labarai Shazali Saleh farawa ya aikowa kadaura24 yace Rasuwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan da shugaban ya tafi kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin shekarar 2022.
A cikin sakon juyayi ga hedikwatar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, da iyalan marigayi Junaidu, Garba Farawa ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma da mutanen kumbotso baki daya.
Yana mai addu’ar Allah s.w.t ya gafarta masa zunubansa, yasa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.