Daga Rukayya Abdullahi Maida
A zaman kotun na yau karkashin jagorancin Mai Sharia Ibrahim Sarki Yola kotun taci gaba da sauraran shari’ar Malam Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara.
Inda Lauyan gwamnati Barista Yakubu Abdullahi ya gabatar da kansa tare da mataimakansa, haka kuma lauyan wanda ake kara wato Barista Dalhatu Shehu ya gabatar da kansa nan take, Lauyan gwamnati ta bakin Barista Abdurrahman Muktar yavfara yiwa malamin tambayoyi ciki kuwa hadda cewar wannan kur’anin da muke anfani dashi cikakkene? Malamin yace kwarai kuwa
Sannan Kuma yayi Masa tambayar cewar menene matsayin karatunsa ? anan ne aka dinga Kai Ruwa Rana daga karshe malamin yace yana da digirin digirgir Wanda yasamu daga hadakar wata jami’ar Amurka dake Ghana, haka kuma malamin anyi masa tambayar Ijaza wato kwalin dake tabbatar da sahihancin iliminsa nanma yace akwai na gidansu da kuma wani malami a kasar Morroco.
Kazalika lauyan gwamnati ya yiwa Abduljabbar tambaya akan cewar suna da wata akida ta cewar Alkurani ba cikakke bane? malamin ya musanta hakan, inda yace shi dai y abada bayani daga cikin wasu littatafai.
Bayani kammala tambayoyinne sai Lauyan Wanda ake tuhuma ya tashi yace yana da magana, bayan da Mai shari’a ya Amin ce masa, sai ya roki kotu data sallami malamin, sannan yace bayanan da aka gudanar kan malamin basu ingantaba don haka ya roki kotun ta sallami malamin ta kuma umarci gwamnati tabashi hakuri da kuma Neman afuwa gareshi.
Ta ke Lauyan gwamnati ya yi suka kan bukatar lauyan Abduljabbar din, yace ya fadi haka ne saboda batun lauyan gwamnati ba shi da muhalli a cikin sashi na 390(2) Amma yana da damar kalubalantar cajin kafin hukunci.
Daga karshe dai kotun ta daga sauraren shari’ar har zuwa ranar 7/7/2022 domin fadar ra’ayinta akan yuwuwar sallamar Wanda ake zargi ko Kuma akasin haka.
Wakiliyar kadaura 24 Rukayya Abdullahi Maida ta rawaito mana cewa lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soran dinki yace ai Babu batun sallama tunda sun gama bada bayanin tuhumar yayin zantawarsa da manema labarai.
Anashi bangaren Lauyan dake Kare malam Abduljabbar wato barista Dalhatu Shehu ya kara tabbatar da rokonsu ga kotu na sallamar Malamin.