NDLEA ta kama gonakin tabar wiwi 5 a Kano

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta gano gonakin tabar wiwi guda biyar a wurare daban-daban na jihar kano.

Kwamandan NDLEA a Kano Abubakar Idris Ahmad ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan da aka gudanar na ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da aka gudanar a Kano.

Ya ce hukumar ta NDLEA a kano tana bakin kokarinta wajen dakile shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran batutuwan da suka shafi hakan a jihar.

Kwamanda Abubakar idris Ahmad ya ce manufar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta waya ita ce wayar da kan jama’a game da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma.

Ya bayyana cewa an gano gonakin tabar wiwi guda biyar a jihar, wadanda suka hada da gona a kauyen Fari dake karamar hukumar Dawakin Kudu, kauyen ‘Yar Bundu dake karamar hukumar Bichi, wani kuma a karamar hukumar Kiru, da wata gonar kuma a dajin Mantau dake karamar hukumar Danbatta. daya kuma a karamar hukumar Nassarawa Gwarzo ta jihar.

Kwamandan ya bayyana cewa rundunar ta samu gagarumar nasara a fannin rage samar da miyagun kwayoyi daga watan Yulin 2021 zuwa Yuni 2022.

“An kama jimillar kilogiram 12.611.656 na haramtattun kwayoyi, wadanda suka hada da kilogiram 9,735.004 na cannabis Sativa, 2,875.223kg na abubuwan psychotropic, 1.123kg na hodar iblis, da 0.128 na Hereon.”

Abubakar Idris Ahmad ya ci gaba da cewa, a tsawon lokacin da rundunar ta kama mutane 1887 ‘yan shekaru 18 zuwa 35,185 ne aka gurfanar da su a gaban kotu, inda aka yankewa mutane 76 hukunci, yayin da ake ci gaba da shari’ar mutane109.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...