An fara shari’ar wasu yan fashi da suka so su yi garkuwa da wani yaro a Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wasu mutane da ake zargi da fashi da makami sun yi barazanar tafiya da dan wani mutum da sukaje gidansa domin fashi shi kuma yai musu turjiya.

An gurfanar dasu a gaban kotun Majistare Mai Lanba 58 karkashin jagorancin Aminu gabari, inda ake tuhumarsu da hada kai da fashi da makami da yunkuurin aikata kisan kai da Samar da mummunan Rauni.

A zaman kotun Lauyan gwamnati Kuma Mai gabatar da Kara Sadik Isa Fara, ya bukaci a karantowa wadanda ake tuhuma laifinsu inda Jamiin kotu Habibu Abdurrahman (Dan boy ) ya karanto musu kunshin tuhumar.

Tunda fari dai Ana zargin Nazir Abdullahi da Tijjani Garba da Aminu Abdullahi da kuma Salisu Abubakar da zuwa unguwar Tudun Fulani suka dinga shiga gida-gida suna yiwa mutane fashi a gidajansu, daga cikin wadanda suka yiwa fashin harda Wanda sukayi garkuwa da dansa dan shekara biyu lokacin da yaki amincewa da bukatarsu haka Kuma Ana zargin sun datsewa wani mutum hannu da adda.

Wakiliyar kadaura 24 Rukayya Abdullahi Maida ta rawaito mana cewa, bayan karanta musu kunshin tuhume- tuhumen sun musanta zagin Wanda daga Nan Kuma kotun ta aike dasu zuwa gidan gyaran Hali har zuwa ranar 27/7/2022 domin sake gabatar dasu don cigaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...