Na biyawa Dalibai 150 kudin Qualifying ne don inganta rayuwar su – Muhd Abba Danbatta

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Babban Sakataren Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano Amb. Muhammad Abba Dambatta ya fara Mika takardun biyan kudin Jarabawar Qualifying Exam ga Dalibai 50 Yan makarantar Govt. Day Arabic Senior Secondary School(Farar Makaranta), form guda 150 da ya Samar ga Dalibai Wadanda suka fadi jarabawar ta samun gurbin zana jarabawar karshe ta S.S.C.E.

Idan za’a ita tunawa a kwanakin baya Babban Sakataren ya tallafawa makarantar ta G.D.A.S.S (Farar Makaranta), da w centre ta zana Jarabawar NECO ga Yan makarantar, a saboda hakanne Abba Danbatta ya baiwa makarantar Kaso mai yawa na adadin wadannan forms fomin makarantar ta samu cikakkiyar amincewa daga Hukumar ta NECO kamar yanda yake a ka’ida.

Sannan Akwai forms guda Dari (100), Su kuma an ware sune ga Wadanda aka zabo daga cikin Dalibai marayu da masu karamin karfi a makarantu daban-daban a yankin.

A jawabinsa Babban Sakataren bayan ya godewa Allah ya yabawa Gwamna Ganduje bisa dama da ya bashi, wacce ita ce ya zama silar allafawa wadannan dalibai .

Abm. Muhd Abba Danbatta ya kuma bada tabbacin zai cigaba da tallafawa rayuwar yara matasa don Su Sami ilimi, don a cewarsa su ne shugabannin gobe, kuma bai kamata shugabannin al’umma su zama basu da ilimi ba.

Ina kira ga sauran al’umma musamman masu mulki da ya masu hannu da shuni da su dauki gabarar tallafawa yara matasa domin su Sami ingantaccen ilimi don inganta rayuwar su”. Danbatta

Shugabannin makarantar da daliban sunyi godiya tare da addu’oi na musamman ga Babban Sakataren bisa wannan Abin alheri da yayi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...