Gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira Biliyan 7 wajen samar da ingantaccen ilimi – Ganduje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da samar da ingantaccen ilimi, Wanda hakan ya jawo domin har a shekarar 2021 ta samu tallafin da ya dace daga hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), sannan kuma a wani bangare na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da ingantacciyar hanyar koyo da koyarwa a makarantunta gwamnatin ta kashe sama da Naira Biliyan Bakwai wajen samar da ingantaccen yanayin koyo a makarantun.

Ganduje ya bayyana cewa, magance kalubalen da ke tattare da matsalar rashin zuwan yara makarantu, na daya daga cikin abin da ya sanya jihar Kano ta fito da dokar ilimin kyauta kuma wajibi musamman a kan ‘yan mata da kananan yara da masu bukata ta musamman duk da yawan dalibai da suke shiga makarantun Jihar.

Gwamnan wanda mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ya bude taron Rabin zango na Hukumar gudanarwa na UBEC tare da shugabannin zartarwa na SUBEB na Kasa a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano.

A cewarsa, manufar samar da shirin ta ta’allaka ne domin magance matsalolin rashin zuwan yara makaranta musamman mata a jihar, inda ya kara da cewa an kashe kudaden masu tarin yawa wajen aiwatar da shirin Ilimi kyauta Kuma dole a jihar kuma Saboda haka ne gwamnati ta kafa Asusun Tallafawa Ilimi don yaba sadaukarwar kudi.

A Sanarwar da babban sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa fagge ya aikowa Kadaura24 yace, Gwamnan ya yaba da gudunmawar Ma’aikatar Ilimi ta kasa da Hukumar Ilimi ta bai-daya da sauran masu ruwa da tsaki suke bayarwa wajen samun ingantaccen ilimi a Jihar Kano.

Ministan Ilimi Mal.Adamu Adamu wanda babban sakataren hukumar UBEC Dr.Hammid Bobboyi ya wakilta ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta ba da fifiko ga ilimin bai daya a Najeriya, Sannan ya bayar da tabbacin gwamnatin za ta ci gaba da magance duk wani abi Kalubale da ya shafi ilimi.

Sai dai ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa gwamnatocin Jihohi ta hannun Bankin Duniya wajen tallafa wa Ilimi mai Kyau ga kowa da kowa (BESDA) don magance matsalar rashin zuwan yara makaranta.

A nasa bangaren, babban sakataren UBEC wanda Farfesa Bala Zakari ya wakilta ya bayyana cewa taron na duk wata kwata-kwata ya taimaka wa UBEC da SUBEB su ci gaba da mayar da hankali kan aikinsu na firamare na samar da ingantaccen ilimi ga yaran da suka isa makaranta a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...