Hadiza Gabon ta Magantu kan batun kin auren Mutumin da ya kaita kara Kotu

Date:

Hadiza Gabon ta musanta batun auren Bala Musa ne bayan da ta gurfana gaban babbar kotun shari’a  dake Magajin Gari a jihar Kaduna, inda ta ce bata taba yi masa alkawarin aure ba, hasali ma bata san shi ba kuma bata da wata alaka da shi ta kusa ko ta nesa.

Tun da fari dai mutumin mai suna Bala Musa ne ya gurfanar da Hadiza Gabon a gaban Kotun, inda ya bukaci a kwato masa hakkin sa, bayan da ya ce ta ki auren sa duk da alkawarin da suka yi, bayan kuma ta cinye kudin sa har naira dubu 396.
Hadiza Gabon ta bakin lauyan ta Mubarak Sani Jibril ta ce tsakanin ta da mutumin bai wuce magoyin bayan ta da suka hadu a shafin ta na Facebook ba, amma babu batun soyayya ko alkawarin aure a tsakanin su.
Ya zuwa yanzu dai mai shari’a Khadi Malam Rilwanu Kyaudai ya dage sauraron karar zuwa tanar 28 ga watan yunin da muke ciki, yayin da ya bada belin Hadiza Gabon, bisa sharadin gabatar da mutane biyu mazauna jihar Kaduna.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa wani ma’aikacin Gwamnatin ya maka Hadiza Gabon a gaban kotu bisa kin aurensa da ta yi bayan ta ci kudinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...