Gyaran Kundin Tsarin Mulki Shi ne Mafita ga Halin da Kasar nan Ke Ciki – Kawu Sumaila

Date:

Daga Zara Jamil Isa

 

 

Tsohon Mataimakin Shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai, Hon. Sulaiman Abdulrahaman Kawu Sumaila ya bayyana cewa akwai bukatar a sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya cikin gaggawa da kuma bada dama ga jihohi da kananan hukumomi wanda hakan zai magance yawancin kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.

Yace shekaru goma 12 da ya yi a Majalisar a karkashin shugabannin Kasa guda 3, ya sa ya fahimci cewa Najeriya na bukatar tsarin da zai taba rayuwar al’umma tun daga tushe Inda yace baiwa Kananan Hukumomi damar cin gashin kansu ita ce mafuta.

Kawu wanda ya kuma yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan majalisar wakilai ta kasar, ya ce, a fahimtarsa akwai matsaloli da yawa da kundin tsarin mulkin kasar nan ya haifar kamar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da matsalolin zamantakewa wanda yace akwai bukatar a sake duba kundin tsarin wanda zai yi dai-dai da buƙatun al’ummar Kasa, wanda ya kira d “Tsarin Mulkin Jama’a”.

Kawu Sumaila Wanda jigo ne a Siyasar Kano kuma yake neman kujerar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari, ya ce Idan ya lashe zaben Zai Mai da hankali wajen gyaran kundin tsarin mulki da kuma yi masa kwaskwarima.

“Idan na zama dan majalisar dattawan Najeriya, zan dage wajen ganin an yiwa kundin tsarin mulkin kasar cikakken nazari da kuma gyara.” Kawu Sumaila

“Kasa mai yawan al’umma kamar Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 200 ace tana da Babban sufeton ‘yan sanda guda daya ko shakka babu dole za’a fuskanci kalubalen tsaro”. Inji Kawu

“Ina goyon bayan samar da ‘yan sandan Jihohi domin sojoji su fuskanci nauyin da tsarin mulki ya dora musu na kare yankinmu, amma hakan na iya faruwa ne kawai idan muka samu ‘yan sandan jahohi ”.

Mu dauki misali jihar Kano, mu kusan miliyan 20 ne, kuma adadin ‘yan sanda a kano bai wuce dubu 8,000 ba, kuma a karamar hukumata ta Sumaila muna da chaji ofis din yan sanda guda biyu, ‘yan sandansu gaba daya ba su wuce 80 ba, a Karamar Hukumar da ta ke da mutane kusan 500,000”. a cewarsa.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta dorawa kanta nauye-nauye Masu yawa, har ma aikin da ya kamata ace kananan Hukumomi ta yi Amma sai ka ga Gwamnatin Tarayyar tana inda ya ce gina cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da Gwamnatin Tarayya tana kamar Gina Asibitocin kula da lafiya a matakin farko Wannan bai dace ba.

Kawu Sumaila ya kuma yi tsokaci kan harkokin ilimi inda ya ce ilimin Jami’a na da matukar muhimmanci kuma dole ne a karfafawa matasa gwiwa su yi shi, ba Wai Kawai su Sami shaidar kammala digiriba, a’a su Sami ingantaccen Ilimi da zasu iya alfahari da shi ko’ina a duniya.

Sai dai yace duk wadannan da ma wasu zasu Samu ne kawai Idan “Muna da kundin tsarin mulki wanda zai sa a sami shugabanci nagari, da rikon amana, yin komai a bide, daina nuna wariya gaskiya, inganci, bin doka da oda da kuma kundin tsarin mulki wanda zai samar da sahihin zabe mai inganci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...