Yanzu-Yanzu APC ta Fitar da sunayen yan takarar data tantance

Date:

Kwamitin mutum-bakwai na tantance ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, John Odigie Oyegun, ya fitar da sunayen mutane 13 daga cikin 23 da jam’iyyar ta tantance.

An mika rahoton kwamitin ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a jiya Juma’a.

Ya shaida wa shugaban jam’iyar na ƙasa cewa an cire sunayen ƴan takara 10 da bisa rashin cancanta.

Daga cikin wadanda kwamitin ya ki amincewa da su sun hada da tsaffin gwamnonin jihohin Imo, Zamfara, da Cross River, Rochas Okorocha, Sani Yerima da Ben Ayade.

Duk da cewa ba a bayyana takardar ba, jaridar Kadaura24 ta samu kwafin mai ɗauke da sunayen waɗanda aka ba da shawarar. Gasu kamar haka:

 

Abubakar, Badaru
Akpabio, Godswill Obot
Amaechi, Chibuike Rotimi
Amosun, Ibikunle
Bello, Yahaya
Fayemi, John Kayode
Jack-Rich. Tein
Lawan, Ahmed
Nwajiuba, Chukwuemeka Uwaezuoke
Ina, Christopher
Osinbajo. Yemi
Tinubu, Asiwaju Ahmed Bola
Umahi, Nweze David

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...