Tawagar Gwamnatin Kano ta ziyarci Waɗanda Iftila’in Gas da guba ya rutsa da su a Asibitin

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Sama da mutane 69 ne aka kwantar a asibitoci daban-daban yayin da wasu yan jaribola suka bude wata tukunyar gas mai dauke da wani sinadarin da ba a san ko menene ba a unguwar Sharada ta jihar Kano.

Shugaban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dr. Hussaini Muhammad, ya ce sama da mutane 69 ne aka kwantar wadanda lamarin ya shafa, Kuma Suna cigaba da karbar wasu.

A halin yanzu wadanda abin ya shafa suna sashen gaggawa na asibitin ana kula da lafiyarsu Sakamakon yadda Suka jikkata, saboda da suke samun sarkewar numfashi ba.

Har yanzu dai ba a gano sinadarin ba amma mutanen yankin sun bayyana cewa yana yaduwa a cikin iska ya yi illa sosai ga mazauna yankin na unguwar mundadu da makwaftan su.

Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da fashewar wata tukunyar gas a unguwar Sheka inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata sama da mutane 19.

 

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji wanda ya jagoranci tawagar jami’an Gwamnatin Kano da suka ziyarci wadanda abin ya shafa a Asibitin, ya ce gwamnati ta himmatu domin samar da kayan agajin gaggawa da kuma biyan kudaden majinyatan.

Sannan ta bayar da umarnin yiwa Waɗanda abun ya shafa Magaji kyauta ba tare da biyan ko sisin Kobo sisi ba, su kuwa Waɗanda gas ya Kona unguwar sheka, Gwamna Ganduje ya bada Umarnin baiwa Iyalan Waɗanda iftila’in ya shafa kudi naira Dubu 50 da Kuma Naira Dubu 100 ga Iyalan Waɗanda suka rasa rayukansu.

Tawagar dai karkashin jagorancin sakataren Gwamnatin Jihar kano Alhaji Usman Alhaji sai Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano Alhaji Usman Bala Gwagwarwa da tsohon Kwamishinan Lafiya Dr Aminu tsanyawa da dai Sauransu Waɗanda suka samu tarba daga Shugaban Asibitin Dr. Hussaini Muhammad

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...