Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Kwamitin tantance yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC Cif John Odigie-Oyegun ya kori mutane 10 daga cikin 23 da suka nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ko da yake ba a kai ga bayyana jerin sunayen wadanda abin ya shafa ba, a halin yanzu kwamitin yana sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin mika rahoton sa ga kwamitin kolin jam’iyyar wanda ke karkashin Sanata Abdullahi Adamu.
Kadaura24 ta rawaito dama dai ana ta kokawa Kan kin bayyanawa al’umma Sakamakon aikin da Kwamitin yayi, kasancewar baifi kwanaki you suka rage a shiga zaben fidda gwani na kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar ba.
Cikakken bayanin na nan tafe….