Dalilan dake Kawo Ciwon Wuya Sanadiyyar Riƙe Wayar salula – Masana

Date:

 

Bijire wa mafi kyawun salon riƙe wayar hannu tsawon lokaci na iya zama sababin ciwon wuya, wasu lokutan ma har da wani irin ciwon kai mai wuyar sha’ani.

Tsokokin wuya masu riƙe da ƙwallon kai na shiga cikin mawuyacin hali gwargwadon yadda aka sunkuyar da ƙwallon kai yayin zama ko tsaiwa.

Nauyin kan mutum ya kai 3Kg zuwa 5Kg. Amma wahalar riƙe nauyin ƙwallon kai ga tsokokin wuya na ƙaruwa da sunkuyawar fuska yayin kallon fuskar wayar hannu ko kuma fuskar kwamfuta.

Saboda haka, sunkuyo da fuska zuwa ƙasa domin kallon fuskar waya ko kwamfuta tsawon lokaci, yana tilasta wa tsokokin wuya ruɓanya aikinsu, yanayin da ke sanya tsokokin shiga cikin hali na matsananciyar gajiya, ɗaurewar tsokokin wuya, ciwon wuya, wasu lokutan ma har da ciwon kai, wanda za ai ta shan magani kuma ya ƙi tafiya.

An fi son riƙe wayar hannu tare da ɗago ta sama dai-dai da fuska ba tare da sunkuyowar fuska ba.

Idan kana fama da ciwon wuya kuma ka sha magani ya ƙi tafiya, tuntuɓi likitan fisiyo domin gano sababi da kuma magance matsalar daga tushenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...