Ba a fahimci kalamaina akan Shugaba Buhari – Tinubu yayi Karin haske

Date:

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar, Bola Tinubu ya ce raina Shugaba Muhammadu Buhari baya daga cikin hayallarsa. Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan tayar da kura da kalaman da ya yi a wata ganawa da ya yi da daliget din APC a jihar Ogun suka yi.

A wajen ganawar ta jiya Alhamis, Tinubu ya ce ba don shi ba da Buhari ya fadi zaben 2015.

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, Tinubu ya ce bai fadi hakan da nufin yi wa Buhari rashin ladabi ba.

Ya ce da yawa ko dai ba su fahimci kalamansa ba ko kuma sun yi musu wata fassara ta daban.

Tinubu ya ce “Ina alfahari da kaina kan rawar da na taka a nasarar da APC ta sha yi. Amma tabbas Shugaba Buhari shi ne babban jagoran nasarar. “Sau biyu ana zabarsa a matsayin shugaban kasa.

Ya jagoranci kasar nan tsawon shekara bakwai, babu mai karyata hakan.

Ban isa na raina abin da ya yi ba ko raina matsayinsa a APC da Najeriya ba,” in ji Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...