Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
A ranar lahadin nan ne ake sa ran Jaruma Ummi Rahab zata angwance da Jarumi Kuma mawakin a masana’antar Kanywood Wato Lilin Baba.
Dama dai al’umma da dama Suna da rade-radin cewa Lilin Baba ba da gaske ne zai auri Jaruma Ummi Rahab ba.
Kadaura24 ta rawaito tuni Karin daurin auren Jaruman biyu yake ta yawo a shafukan Sada zumunta kamar haka:
Haka zalika tuni hotunan kafin aure na amarya Jarumar Kannywood Ummi Rahab Da Mawaƙi Lilin Baba Suma suka karade shafukan Sada zumunta musamman Facebook da integram.
Allah Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya da zuri’a ɗayyibah Ameen