Mu muka yankewa APC cibiya, Babu abun da zai sa na barta – Sanata Shekarau

Date:

Daga Nauwara Ahmad Sahel

Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya musanta labarin da ake yadawa cewa zai fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP ko NNPP.

Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne Cikin Wata sanarwa da ya fita a Sahihin shafinsa na Facebook a daren jiya lahadi.

Ga cikakkiyar Sanarwar :

INA CIKIN JAM’IYYAR APC DARAM-DAM

Assalamu alaikum

Ina yi wa dukkan al’ummar Najeriya Barka da Shan Ruwa. Ina fata Allah SWT ya karbi ibadunmu.

A kwanakin nan na goman karshe a Ramadan muna rokon Allah ya sada mu da wannan dare mai daraja na Lailatul Qadri.

“Daga safiyar jiya zuwa yammacin yau Lahadi 24 ga watan Afrilu 2022 na samu sakonni daga wurare da yawa, suna tambayar matsayina dangane da halin da ake ciki a jam’iyyar mu ta APC”.

“Labaran da ake yadawa cewa ina shirin canza sheka zuwa wata jam’iyya ba gaskiya bane. Ni Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano ina nan a cikin jam’iyyar APC, babu wani shiri ko kulli a sarari ko a boye na shiga wata jam’iyya ta daban”.

Ya kamata jama’a su sani jam’iyyar APC dani aka yanke mata cibiya, kuma nayi aiki tukuru domin samun kafuwarta da nasararta. Yadda ake tafiyar da ita ne muke jayayya aka kai, kuma maganar tana gaban kotu. Har yanzu muna sauraren hukuncin karshe na kotun koli.”

“Ina fatan zaku ci gaba da yi mana addu’a ta alheri da fatan dorewar zaman lafiya a Kano da Najeriya.”

A makon da ya gabata ne dai akai ta yada labarin cewa Malam Ibrahim Shekarau yace Wai daga Abuja zai tsaya a na’ibawa Yan Lemo ,Wanda akai ta alakanta hakan da cewa jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari yace shirin komawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...