Jami’an tsaro a Makkah sun kama masu barace-barace a Harami

Date:

 

Hukumomin tsaro a Saudi Arebiya sun sanar da kama ƴan ƙasa da masu karya doka, har da ma wasu masu barace-barace a Masallacin Harami na Makka.

Hukumomin sun baiyana cewa sun kama wani ɗan ƙasar india da ya ke marairaice wa masallata domin su bashi sadaka, inda su ka kame wani ɗan ƙasar Morocco ya na bara kai tsaye, dukkan su a Masallacin Harami na Makka.

Sun ƙara da cewa sun kama wani ɗan Yemen da ya ke basaja da sandar guragu, a zuwan shi gurgu ne domin a bashi sadaka.

Hakazalika, hukumomin sun ce sun kama wani mahaifi yana basaja da ɗan sa da ya ɗora a kan keken guragu cewa bashi da lafiya domin a basu sadaka, amma da a ka kama shi, sai a ka ga ɗan nasa lafiyayye ne.

Hakan na zuwa ne bayan da Saudi Arebiya ta saka dokar mai karfi ta hana bara.

Tuni mahukunta a ƙasar su ka fara kamen mabarata a wani matakin na tabbatar da hana karya dokar hana barace-barace ta ƙasar.

Duk wanda a ka kama ya na barace-barace da makamantan irin waɗannan laifukan sai an ɗaure shi shekara ɗaya a gidan yari ko kuma ya biya tarar Riyal dubu 100.

Kadaura24 ta gano cewa waɗanda hukumomin su ka kama na bara ba ƴan Nijeriya ba ne, saɓanin rahotanni da ke fitowa a shekarun bayan cewa ƴan Nijeriya, musamman Hausa wa na zuwa Saudiya domin yin bara su samu kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...