Ramadan: Bola Tinubu ya saukewa kungiyoyi a Kano kabakin arziki

Date:

Daga Mubaraka Aliyu Ibrahim

Mai Neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar Shugaban kasa a zabe Mai zuwa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya rabawa Kungiyoyin a Kano buhunhunan shinkafa domin tallafa musu a Wannan lokaci na Ramadan.

Tsohon Kwamishinan matasa da wasanni na jihar kano Alhaji Kabiru Ado lakwaya, Wanda shi ne Shugaban Kwamitin rabon Kayan sh ne ya bayyana hakan yayin Kaddamar da rabon Kayan a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Tsohon Kwamishinan yace Bola Tinubun ya raba Kayan ne domin tallafawa al’ummar Jihar kano a kokarin da yake na saukakawa Rayuwar al’umma Musamman a wannan lokaci na Ramadan.
Yace za a raba kayan ne ga kungiyoyi daban-daban dake jihar Nan,Inda aka raba musu kanana da Manyan buhunhunan shinkafa har Dubu daya da dari takwas.
Wasu daga cikin Waɗanda Suka amfana da tallafin sun godewa Bola Ahmad Tinubu bisa Wannan tallafi da ya baiwa Rukunonin Kungiyoyi daban-daban dake jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...